QUOTES ON #RAMADĀN_MUBĀRAK

#ramadān_mubārak quotes

Trending | Latest
7 MAY 2021 AT 8:17

Allaah Ya na saukowa izuwa sama ta daya a dukkan qarshen daya bisa ukun kowanne dare domin Ya amsa addu'o'in bayinShi. A yayin da muke sallah muna yin munajati da Allaah ne kai tsaye, saboda haka mu roqe Shi dukkan buqatan mu Shi kuma Zai amsa mana, musamman a wadannan kwanakin masu tsada.
Allaah Ya amsa dukkan buqatun mu na alheri.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_BIYAR

-


1 MAY 2021 AT 9:09

Shin, kana ta addu'a ba'a amsa maka ba? To kwantar da hankalinka dan uwa, kada ka fidda rai, domin babu wata addu'a da zakayi Allaah bai amsa maka ba, saboda Allaah Yana kunyar bawan shi ya daga hannu har ya sauke ba tare da Ya amsa mashi addu'ar shi ba. Ta yiwu abinda ka buqata ba alheri bane a baka shi a wannan lokacin, ko kuma Allaah cikin ikonShi Ya maye maka da abinda ya fi shi alheri.
Abinda ake so da mumini a yayin addu'a, shi ne ya kasance kana da YAQININ Allaah Zai amsa maka sa'annan kuma kayi HAQURI.
Allaah Ya sanya mu cikin bayinShi da suke kyautata maShi zato.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_SHA_TARA

-


11 MAY 2021 AT 8:33

Watan Ramadāna dai yana mana bankwana. Sai mai tsananin rabo ne zai ga wasu Ramadānan.
'Yan uwa kada mu dauki wannan watan a matsayin lokacin saurarawar zunuban mu. Mu jajirce matuqa wajen ganin cewa mun qaurace zunuban mu matuqar qauracewa, ta haka ne zamu cimma babbar manufar yin azumi, wato samun tsoron Allaah (Taqwa).
Yana daga cikin alamar aikin mutum ya kar6u shine mutum zai ga aikata wannan aikin yana mashi sauqi da kuma tabbatuwa akan hakan.
Allaah Ya amsa ibadun mu, Ya yafe mana kurakuran mu, Ya kuma bamu tsawon rayuwa mu azumci Ramadāna a shekaru da dama masu zuwa.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_TARA

-


22 APR 2021 AT 4:04

SubhānAllāh!!! Cikin ikon Allaah kamar jiya muka fara azumi amma yau ga shi har mun ci daya bisa ukun watan Ramadāna. Hakan yana nuna mana yadda lokaci yake gudu sosai.
Abin lura anan shine, shin muna amfani da lokutan mu wajen yin abinda ya dace? Idan amsar mu a'a ce, to fa bamu makara ba, muna da sauran lokacin da zamu gyara wannan kuskuren.

Allaah Ya bamu ikon amfani da lokutan mu wajen Yi maShi da'a.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_GOMA

-


12 MAY 2021 AT 8:39

A yayin da wasu daga cikin 'yan uwa Allaah Ya kar6i rayukansu, wasu kuma suna kwance babu lafiya, sai akayi sa'a mu kuma gashi mun dauki azumin qarshen wannan shekara cikin qoshin, kuma ma muna sa ran mun dace da daren Laylatul Qadari, haqiqa wajibi ne mu yiwa Allaah godiya, Alhamdulillaah.
Allaah Ya jiqan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, Ya bawa marasa lafiyar mu lafiya, Ya kuma maimaita mana muna masu rai da qoshin lafiya.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_TALATIN

-


30 APR 2021 AT 5:32

Kamar yadda muke gani kwanakin watan Ramadāna sai shudewa suke a hankali. Da wannan ne nake kira gare mu, da mu kiyaye lokacin mu, kuma muyi amfani da shi wajen ayyukan alheri.

Allaah Ya bamu ikon yin tuntuntuni domin qara qaimi wajen yi maShi da'a.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_SHA_TAKWAS

-


29 APR 2021 AT 4:29

Idan har bamu iya qauracewa zunubai a yayin da shaidanu suke daure a watan Ramadāna ba, to tabbas munfi su kansu shaidanun shaidanci da shu'umanci.

Allaah Ya bamu ikon kamewa daga barin sa6a maShi, Ya kuma daukaka darajar mu.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_SHA_BAKWAI

-


8 MAY 2021 AT 9:06

Ibn Qayyim Al-Jauziyyah yana cewa:

"Abinda ya gabata tamkar mafarki ne,
Abinda ake muradi (nan gaba) gaibu ne,
Amma a tare da kai
Kana da sa'a (hour) wanda shine lokacin da kake ciki (yanzu)."

Sa'a anan zamu iya danganta shi da kwanaki goman qarshen watan Ramadāna. Sune sa'o'in (hours) da muke dasu a hannun mu, su muke muradi, saboda haka sai muyi iya qoqarin mu wajen ganin cewa mun amfane su.
Allaah Ya datar damu da daren Laylatul Qadari.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_SHIDA

-


6 MAY 2021 AT 8:31

Wasu daga cikin mu suna da dabi'ar bayyanawa mutane wata ibada da sukayi a 6oye musamman sallar dare (TAHAJJUD) domin mutane su yaba musu (RIYA). To wallaahi mu kula, duk wani aiki da zamuyi na ibada matuqar ba yardar Allaah kadai muke nema ba to 6ata lokaci ne kawai, ba ma 6ata lokaci kadai ba har fushin Allaah hakan zai jawo mana. Saboda haka a duk lokacin da zamu bautawa Allaah to ya kasance mun tsarkake niyyar mu.

Allaah Ya bamu ikon yin ibada don neman yardarSa kadai.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_HUDU

-


10 MAY 2021 AT 8:45

Magabata na qwarai sun kasance suna kuka a duk lokacin da kwanakin Ramadāna suka zo qarshe, saboda sun san ba lallai su samu damar kaiwa shekara mai zuwa ba. Ko kuma ka same su suna masu alhinin rabuwa da alkhairan da babu su a sauran watannin da ba Ramadana ba.
Amma abin takaici akasin haka ne yake faruwa a wannan zamanin, har alla-alla muke watan ya wuce, ji muke kamar wani babban nauyi ne aka dora mana, mun manta Allaah Bai ta6a dorawa bawanShi abinda bazai iya ba.

Allaah Ya bamu ikon son bauta maShi, Ya kuma tabbatar da mu akan hakan.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_TAKWAS

-