Muhammad Uznulkhair Bala   (Muhammad Uznulkhair)
8 Followers · 3 Following

Joined 5 April 2019


Joined 5 April 2019
27 MAR 2024 AT 3:20

In the abyss of swirling blue,
A solitary figure, lost in hue.
Beneath the waves, his struggles wane,
An echo of despair, a silent pain.

His arms reach out, grasping air,
As currents pull with relentless flair.
In the depths, where shadows dwell,
His silent plea, a haunting knell.

A dance with fate, a struggle vain,
A heart's lament, a soul's refrain.
Yet in the depths, a glimmer shines,
Hope's whispered promise, amidst the brines.

With each breath stolen by the sea,
A prayer rises, wild and free.
For in the darkest depths, he finds,
A strength within, a spirit that binds.

Though waves may crash, and tempests roar,
He'll rise above, and shore to shore,
For in the depths, a truth is clear,
Even in darkness, light draws near.

-


9 JUN 2023 AT 0:18

I have a firm belief that God will not burden me with that which I can't handle. God, please grant me more strength to overcome every trial You may test me with 🙏🏾

-


9 JUN 2023 AT 0:14

I have a firm belief that God will not burden me with that which I can't handle. God, please grant me more strength to overcome every trial You may test me with 🙏🏾

-


12 MAY 2021 AT 8:39

A yayin da wasu daga cikin 'yan uwa Allaah Ya kar6i rayukansu, wasu kuma suna kwance babu lafiya, sai akayi sa'a mu kuma gashi mun dauki azumin qarshen wannan shekara cikin qoshin, kuma ma muna sa ran mun dace da daren Laylatul Qadari, haqiqa wajibi ne mu yiwa Allaah godiya, Alhamdulillaah.
Allaah Ya jiqan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, Ya bawa marasa lafiyar mu lafiya, Ya kuma maimaita mana muna masu rai da qoshin lafiya.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_TALATIN

-


12 MAY 2021 AT 8:36

A yayin da wasu daga cikin 'yan uwa Allaah Ya kar6i rayukansu, wasu kuma suna kwance babu lafiya, sai akayi sa'a mu kuma gashi mun dauki azumin qarshen wannan shekara cikin qoshin, kuma ma muna sa ran mun dace da daren Laylatul Qadari, haqiqa wajibi ne mu yiwa Allaah godiya, Alhamdulillaah.
Allaah Ya maimaita mana muna masu rai da qoshin lafiya.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_TALATIN

-


11 MAY 2021 AT 8:33

Watan Ramadāna dai yana mana bankwana. Sai mai tsananin rabo ne zai ga wasu Ramadānan.
'Yan uwa kada mu dauki wannan watan a matsayin lokacin saurarawar zunuban mu. Mu jajirce matuqa wajen ganin cewa mun qaurace zunuban mu matuqar qauracewa, ta haka ne zamu cimma babbar manufar yin azumi, wato samun tsoron Allaah (Taqwa).
Yana daga cikin alamar aikin mutum ya kar6u shine mutum zai ga aikata wannan aikin yana mashi sauqi da kuma tabbatuwa akan hakan.
Allaah Ya amsa ibadun mu, Ya yafe mana kurakuran mu, Ya kuma bamu tsawon rayuwa mu azumci Ramadāna a shekaru da dama masu zuwa.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_TARA

-


10 MAY 2021 AT 8:45

Magabata na qwarai sun kasance suna kuka a duk lokacin da kwanakin Ramadāna suka zo qarshe, saboda sun san ba lallai su samu damar kaiwa shekara mai zuwa ba. Ko kuma ka same su suna masu alhinin rabuwa da alkhairan da babu su a sauran watannin da ba Ramadana ba.
Amma abin takaici akasin haka ne yake faruwa a wannan zamanin, har alla-alla muke watan ya wuce, ji muke kamar wani babban nauyi ne aka dora mana, mun manta Allaah Bai ta6a dorawa bawanShi abinda bazai iya ba.

Allaah Ya bamu ikon son bauta maShi, Ya kuma tabbatar da mu akan hakan.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_TAKWAS

-


9 MAY 2021 AT 8:39

Daren Laylatul Qadari dare ne da yake cike da taskokin alkhairan Allaah. A wannan dare ne mala'iku suke saukowa da dukkan abinda Allaah Ya qaddara na wannan shekarar tare da izinin Shi.
Wannan dare an lullu6e shi da wata nutsuwa da kwanciyar hankali na musamman har sai alfijir ya keto.

Ubayyu Bin Ka'ab yace "Yana daga alamar wannan dare shine washegarin wannan dare ranar tana hudowa ba tare da harshen haskenta (sun rays) ba.
Wannan dare ne da dukkan muminai suke muradi.
Muna roqon Allaah Ya sa mu dace da ganin wannan dare.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_BAKWAI

-


8 MAY 2021 AT 9:06

Ibn Qayyim Al-Jauziyyah yana cewa:

"Abinda ya gabata tamkar mafarki ne,
Abinda ake muradi (nan gaba) gaibu ne,
Amma a tare da kai
Kana da sa'a (hour) wanda shine lokacin da kake ciki (yanzu)."

Sa'a anan zamu iya danganta shi da kwanaki goman qarshen watan Ramadāna. Sune sa'o'in (hours) da muke dasu a hannun mu, su muke muradi, saboda haka sai muyi iya qoqarin mu wajen ganin cewa mun amfane su.
Allaah Ya datar damu da daren Laylatul Qadari.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_SHIDA

-


7 MAY 2021 AT 8:17

Allaah Ya na saukowa izuwa sama ta daya a dukkan qarshen daya bisa ukun kowanne dare domin Ya amsa addu'o'in bayinShi. A yayin da muke sallah muna yin munajati da Allaah ne kai tsaye, saboda haka mu roqe Shi dukkan buqatan mu Shi kuma Zai amsa mana, musamman a wadannan kwanakin masu tsada.
Allaah Ya amsa dukkan buqatun mu na alheri.

#RAMADĀN_MUBĀRAK
#RANA_TA_ASHIRIN_DA_BIYAR

-


Fetching Muhammad Uznulkhair Bala Quotes